Wani Magidanci Ya Ɗaure Matansa 2 Da Mari Tsahon Shekara Ɗaya A Katsina

1171

Rundunar Yansandan jihar Katsina ta sanar da kama wani mugun magidanci mai suna Samaila wanda ake zarginsa da cin zarafin matansa guda biyu ta hanyar dauresu da kaca tsawon wata da watanni.

Magidanci mai suna Samaila mazaunin kauyen yan Nabaiyye da ke cikin karamar hukumar Rimi ta jahar Katsina, ya daure matan nasa biyu da suka hada da Fatima Salisu da Hadiza Musa, wanda shekarunsu basu wuce ashirin ashirin ba.

Kakakin Rundunar ƴan sandan SP Gambo Isah, ya ce Samaila ya daure matan na sa ne tsawon watanni 10.

A nata ɓangaren Mahaifiyar Hadiza ce ta fara gano halin da diyarta da abokiyar zamanta suke ciki yayin wata ziyara da ta kai gidanta ba tare da sanar da ita ba, inda ta tafi daukan keken dinkin da ta sayawa diyarta, amma sai mijin ya hanata dauka, hakan yayi sanadiyar cacar baki tsakaninsu, inda ya doketa.

Wannan ne yasa matar ta garzaya ofishin Yansanda dake cikin karamar hukumar Rimi domin kai korafi, daga nan sai Yansanda suka gayyaci Samaila domin amsa tambayoyi, sai dai basu gamsu da bayanansa ba, don haka suka tafi gidansa domin gudanar da bincike.

A sanadiyyar wannan bincike ne Yansanda suka gano matan biyu daure da kaca cikin mawuyacin hali har sun fita hayyacinsu, haka zalika yansanda sun gano manyan mari, layoyi da kuma muggan makamai.

A cewar Fatima, bayan Samaila ya dauresu, sa’annan ya aske musu gashin gaba da kuma yanke musu kumba wanda yayi amfani dasu wajen hada wani jiko, kuma ya tilasta musu su sha.

“Samaila baya barinmu mu fita ko ina, a daure muke fitsari muke kashi, baya kwancemu sai lokacin da yake bukatar saduwa damu, haka muke kallo a duk lokacin da yake saduwa da wani daga cikinmu, haka zalika yana dukanmu da wayar wuta.” Inji ta.

Bugu da kari Hadiza ta ce Samaila baya son jin lokacin da muke jinin haila, saboda a duk lokacin daya gane muna jinin haila duka ne zai biyo baya tare da barazanar kashe mu, sai dai tace basu san sana’arsa ba, amma dai suna ganinsa kullum yana dawowa gida da yan dari biyar biyar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan