Yau Ake Bikin Ranar Hijabi Ta Duniya

1402

Ranar ɗaya ga watan Fabrairu, kowacce shekara ne ake bukin ranar sanya hijabi, wanda ya samo asali daga wata mazauniyar New York, a kasar Amurka, mai suna Nazma Khan.

Ita ta fara wayarwa matan duniya kai ta hanyar sadarwar yanar gizo, wato {Internet} wanda hakan ya ja hankalin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba a kasashen duniya.

An fara bukin wannan ranar ce a shekara 2013, don jan hankalin matan duniya, wajen sujurta jikinsu da kuma kwadaita masu sa hijabi, koda sau daya ne domin gani yadda girmama mace yake a Musulunci.

Sama da kasashe 140 ne ke raya ranar Hijabi ta duniya, ta hanyar taron lakcoci da fadakarwa akan amfanin sanya hijabi

Daga cikin muhimamn abubuwan da ake tunatar da mata a kansu a wannan rana har wayar da kansu kan muhimmancin da ke tattare da saka hijabi da tasirinsa wajen kare muuncin mace.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan