Siyasar Kano: Ina Makomar Farfesa Hafizu Abubakar?

285

A kakar zaben shekarar 2019 siyasar jihar Kano ta dauki wani sabon salo da masharhanta da dama suka karkatar da alkalumansu a game da yadda siyasar jihar ta Kano ta rika gudana.


Tun a shekarar 2016 ne a watan Maris rigimar siyasa ta barke tsakanin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje.


Wannan sabon salo da siyasar ta jihar Kano ta dauka yasa shugabannin majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin tsohon shugaban majal isar Kabiru Alhasan Rurum suka bukaci Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya cire jihar hula.

A lokacin mafi rinjaye na ‘’yan majalisar ta jihar Kano sun cire jihar hula banda ‘’yan tsiraru daga ciki.


Amma lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake mayar da jawabi ya nemi ‘’yan majalisar ta jihar Kano da su yi masa afuwa shi da tsohon mataimakin sa Farfesa Hafizu Abubakar na su cigaba da saka jar hular har zuwa wani lokaci.


Hakan akayi ta tafiya, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na saka jar hula shi da mataimakinsa har zuwa karshen shekarar 2018.


Amma kafin akai karshen shekarar 2018 din ce mataimakin gwamnan na jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar, ranar 4 ga watan Agusta ya sanar da cewa yayi murabus daga kan kujerar mataimakin Gwamna.


Dalilin haka ne ya saka kujerar ta zama babu kowa har zuwa lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tura sunan Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya maye gurbin Farfesa Hafizu Abubakar.

Jim kadan bayan sanarwar Murabus din da yayi, sai Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana komawar sa jam’iyyar PDP inda ya gayawa manema labarai a cibiyar bincike da harkokin nazarin Dumkradiyya ta Mambayya cewa ya bi jagoransa a siyasa wato Injinya Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar PDP.


Farfesa Hafizu Abubakar ya koma gidan siyasa na Kwankwasiyya lokacin da ake shirin fitar da ‘’yantakarar gwamna.


Bayan da aka yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP sai Abba Kabiru Yusuf da Kwamared Aminu Abdussalam suka bayyana a matsayin ‘’yan takarar gwamna da mataimaki.


Hakan ta saka wasu ‘’yan takarar na gwamna da suka hada da shi Farfesa Hafizu Abubakar da Malam Salihu Sagir Takai da Architect Aminu Abubakar Dabo da marigayi Sanata Isah Yahaya Zarewa suka bar jam’iyyar ta PDP.

Barinsu jamiyyar ta PDP wasunsu, irin su Architect Aminu Abubakar Dabo da Sanata Isa Yahaya Zarewa suka koma jam’iyyar APC.


Amma Farfesa Hafizu Abubakar tare da Malam Salihu Sagir Takai sun koma jam’iyyar PRP mai mukulli.


Jamiyyar PRP ta tsayar da Malam Salihu Sagir Takai a dantakarar ta na Gwamna,sannan daga baya Farfesa Hafizu Abubakar ya sake komawa wata jamiyyar duk a tsakanin murabus dinsa zuwa zaben shekarar bara ta 2019.

Daga baya kuma Farfesa Hafizu Abubakar ya sake komawa jami’yyar APC, ,sannan daga bisani ya daina saka jar hula da aka saba ganin sa da ita.


Tsohon mataimakin gwamnan na Kano bayan komawar sa jamiyyar ta APC ,gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya jagoranci ce su da shi da Architect Aminu Abubakar Dabo da Marigayi Sanata Isa Yahaya Zarewa inda suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.


Kafin da bayan kammala zaben shekarar bara ne dai Farfesa Hafizu Abubakar ya rika bayyana a taruka da dama na jam’iyyar APC wanda ya hada da taro Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yazo yakin neman zabe jihar Kano.


Bayan haka yana bayyana a abubuwa da dama da suka shafi harkokin gwamnatin jihar Kano da gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, sannan ya taba kaiwa magajin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna ziyara ofishinsa.


Shi kansa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taba daukar tawagar manyan ‘’yan siyasa kafin zabe sun kai ziyara gidan Farfesa Hafizu Abubakar ,daga ciki har da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Sanata Malam Ibrahim Shekarau da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas.


Duk da hakan jama’a na ta dakon su ga shin a siyasance musamman ma a jami’yyar ta APC dake mulkin jihar Kano da na tarayyar Najeriya me Gwamnati zata yiwa Farfesa Hafizu Abubakar.


A matsayin sa na kwarraran Farfesa akan lafiyar abinci anyi dako a ga kowanne matsayi shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bashi bayan komawa kan karagar mulki amma shiru kake ji.

Hatta sanda shugaba Buhari ya kai sunayen ministoci wasu sun yi hasashen su ga ko da sunan Farfesa Hafizu Abubakar, sai kwatsam ga sunan Alhaji Sabo Nanono da Manjo Janar Bashir Salihi Magashi.


Masu sharhin al’amuran yau da kullum na ganin cewa a jihar Kano indai ba mukamin Gwamna Farfesa Hafizu Abubakar zai samu ba, sai dai ka mayar da shi mukamin sa na mataimakin Gwamna wadda a yanzu akwai wanda yake kanta.


Duk mukamin da aka bawa Farfesa Hafizu Abubakar sabanin Gwamna ko mataimakin sa a jihar Kano ci baya ne gare shi a siyasa.

Abbas Yusha’u Yusuf Ɗan Jarida ne, ya rubuto daga Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan