Mota Mai Tashin Tsuntsaye Za Ta Fara Shawagi A Shekarar Bana

356


Kimanin shekaru goma sha biyar 15, ke nan da wani kamfanin kasar Israel, “Cormorant” da suka fara wani yunkuri na kera mota mai tsashi sama, kamar angulu. Zuwa yanzu, suna sa ran nan da shekarar 2020, wannan motar, mai suna “Urban Aeronautics” zata fara tashi sama.

Motar dai zata iya daukar kaya masu nauyin da ya kai kimanin kilo gram dari biyar 500kg, dai-dai da nauyin buhun siminti goma 10, wannan motar zata dinga tashi kamar jirgi mai saukan angulu.

Kuma zata iya tafiya da ta kai kimanin kilomita dari da tamanin da biyar 185, kimanin nisan daga Abuja zuwa Kano, cikin awa daya.

An dai kiyasta yawan kudin siyan motar, da zata iya kaiwa dallar Amurka milliyan goma sha hudu $14M, dai-dai da naira billiyan hudu da milliyan dari biyu. Motar dai bata da wani abu, da yake kama da jirgi mai saukar angulu, domin bata da fankokin sama.

Za kuma a iya amfani da motar wajen shiga cikin sunkurun wurare, don magance wasu matsaloli, ko wajen kai dauki da agaji, wanda shigan mota mai tafiya a kasa zai yin wuya. Za’a iya amfani da motar wajen kai agajin gaggawa a cewar shugaban kamfanin Mr. Rafi Yoeli

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan