A cikin shekara Biyu, Ma’aurata 53 Sun Rasa Rayukansu A Hannun Abokan Zamansu

113

A ƙalla ma’aurata 53 ne ake zargin abokan zaman su sun kashe su a Najeriya zuwa yanzu, tun daga 19 ga watan Nuwamba, 2017, lokacin da Maryam Sanda ta kashe mijinta, kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna.

Wata 26 bayan ta kashe mijinta, sai a kwanan ne aka yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ce ta gurfanar da ita a gaban kotu ranar 24 ga Nuwamba, 2017 bisa mutuwar mijinta, Biliyaminu Bello, ɗa ga tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Bello Halliru Muhammad.

Da yake yanke hukunci a kan ƙarar a ranar Litinin da ta gabata, alƙalin da ya saurari ƙarar, Mai Shari’a Yusuf Halilu ya ce hujjar da wadda aka tabbatar da laifinta cewa mamacin ya mutu ne bayan da ya faɗa a kan kwalbar Shisha kawai wata hujja ce ta ƙoƙarin rikita kotu.

Ya tabbatar da cewa a ƙarƙashin ƙa’idar da ake kira ‘Doctrine of Last Seen’, ya zama wajibi wadda aka tabbatar da laifin nata ta yi bayanin musabbabin rasuwar mamacin, ba wai masu ƙara ba, tunda ta yadda cewa ita ce mutum ta ƙarshe da aka gani tare da mamacin.

Labarin Misis Sanda da Mista Biliyaminu ɗaya ne kawai daga cikin labaran mace-macen ma’aurata da ake ci gaba da samu a hannun abokan zaman su a ‘yan shekarun nan.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ogun ta cafke wani mutum ɗan shekara 40 mai suna Bamidele Olanrewaju, bisa zargin sa da dukan matarsa har ta mutu.

Wannan al’amari, a cewar sanarwar da Mai Magana da Yawun Rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ya afku ne ranar Lahadi, 19 ga Janairu, 2020 a gidan da waɗannan ma’aurata ke zaune a ƙauyen Bisodun dake kan hanyar Ofada, a ƙaramar hukumar Obafemi-Owode.

Wanda ake zargin ya yi amfani da wata ƙatuwar sanda ne inda ya doki matar tasa har ta suma, bayan nan kuma ya caka mata sukundireba a kanta, abinda ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Haka kuma, wani mutum ɗan shekara 60 a Ile-Ife dake jihar Osun, Rafiu Irawo, ya kashe matarsa, Funke, kuma ya kashe kansa bisa zargin matarsa da yin lalata da wani mutum.

Wannan al’amari ya afku ne a yankin Alakowe dake Ille-Ife ranar Juma’a, 20 ga Satumba, 2019.

Haka kuma, an zargi wata mata mai suna Akorede Balogun da laifin kashe mijinta, Rasaki Balogun, wanda aka same shi a mace tare da matar da karuwarsa, Muyibat Alabi a gidansa mai lamba 16 dake Taiwo Oke Street, Victory Estate, Ejigbo a jihar Lagos ranar 10 ga Yuli, 2019.

Wani shaida, Oguegbu Promise, ya faɗa wa manema labarai cewa da ƙarfi Misis Balogun ta zuba wani abu mai ruwa-ruwa, wanda ake zargin guba ce a bakin mamacin.

Haka kuma, Rundunar ‘Yan Sandan ta Jihar Ogun ta ƙara cafke Mutiu Sonola, ɗan shekara 37 bisa zargin sa da dukan matarsa ‘yar shekara 34, Zainab Shotayo har ta mutu.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne ranar Laraba, 25 ga Disamba, 2019 biyo bayan rahoto da mahaifin mamaciyar ya shigar, wanda ya kai rahoto a ‘Ibara Division’ na rundunar.

Wani al’amarin ya sake faruwa kwanan nan ranar 27 ga Janairu, 2020 da ƙarfe 4:00 na dare lokacin da aka zargi wata mata ‘yar shekara 19, Rabi Shamsudeen ta hallaka mijinta ɗan shekara 25, Shamsudeen Salisu a ƙauyen Danjanku dake ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

Wannan al’amari ya afku ne sakamakon rashin fahimta a tsakanin waɗannan matasan ma’aurata, a cewar wani rahoto.

Maƙobta, waɗanda suka ce sun ji mamacin yana kuka a kawo taimako, sun garzaya wajen suka same shi yana birgima a wajen ɗakin, kuma jini yana zuba daga wani rauni da ya samu a cikinsa.

An ce sun ga matar mamacin a kusa da shi, tana riƙe da wuƙa, ga jini a jikin wuƙar.

An ce wasu maƙobta sun garzaya da mamacin zuwa asibiti inda likitoci suka ce ya mutu.

An samu rahotannin afkuwar irin waɗannan kashe-kashe a dukkan faɗin ƙasar nan.

Binciken Daily Trust ya nuna cewa mata 36 sun rasa rayukansu a hannun mazajensu, yayinda maza 17 suka rasu rayukansu a hannun matayensu.

Wannan abin damuwa ne ƙwarai da gaske, kuma tuni ‘yan Najeriya sun fara nuna damuwarsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan