Home / Labarai / An Yankewa Wani Mutum Hukuncin Ɗaurin Shekaru 18 Akan Laifin Tofa Yawu Cikin Abinci

An Yankewa Wani Mutum Hukuncin Ɗaurin Shekaru 18 Akan Laifin Tofa Yawu Cikin Abinci

Alkalin garin Eskisehir dake ƙasar Turkiyya ya yankewa wani ma’aikacin sufurin abinci hukuncin daurin shekaru goma sha takwas a gidan yari akan laifin tofa yawu da ya yi a cikin abincin pizza gabanin ya baiwa wanda ya saya.

Lamarin ya faru ne a shekarar 2017 inda kyamarar tsaro ta dauki bidiyon mai sufurin abincin daga gidajen abinci zuwa gidajen masaya, yayin da yake tofawa abincin Pizza yawu gabanin ya sallamawa wanda ya yi ordar abincin ya mika masa.

Mai sufurin abincin mai suna Burak S ya rinka tofa yawu cikin abincin yana kuma daukar bidiyon abinda yake yi da wayarsa.

Da farko dai masayin abincin ya nemi abiya shi diyyar kudin Turkish Lira 500,000 daga gidan abincin da hakan ya faru, kasancewar rashin amincewa da gidan abincin bai yi ba ya sanya shi kai kara a kotu.

Alkalin ya zargi mutumin da lalata abinci barna da kuma sanya guba a abincin da wani zai ci.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *