Gwamnatin Buhari Ta Gurfanar Da Manoma Dubu 70 A Gaban Kotu

206

Gwamnatin tarayya ta shigar da karar manoman jihar Kebbi guda dubu 70 a gaban kotu, bayan da suka gaza biyan Naira biliyan 17 da suka karba a matsayin aro daga gwamnati.

Cikin watan Nuwambar shekarar 2015 ne, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri mai taken ‘Anchor Borrower’ karkashin jagorancin Babban Bankin Kasar nan a jihar Kebbi, inda gwamnatin tarayyar ta tallafawa manoman da kudaden na aro.

Cikin wata zantawa da jaridar Daily Trust, shugaban kungiyar manoman shinkafa ta RIFAN na jihar Kebbi, Muhammad Sahabi ya bayyana cewar, a halin da ake ciki manoma 200 ne kacal suka mayar da rancen da suka karba.

Shugaban manoman shinkafar ya kara da cewar kafin kaddamar shirin bada bashin noman na Anchor Borrower a 2015, manoman jihar Kebbi na noma adadin ton dubu 70 ne shinkafa a shekara, amma bayan kaddamar da shirin, adadin shinkafar da suke nomawa ya karu a 2016 zuwa ton miliyan 1 da dubu 200 a shekara guda.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan