Hali 7 Da Al’ummar Arewacin Najeriya Su Ke Ciki

43

Su ke da shugaban ƙasa dan yankinsu, kuma Musulmi, amma sun fi ‘ya’yan sauran yankunan fuskantar zilla, kisa, talauci da garkuwa da mutanensu.

Kiristocinsu suna nuna wa Musulminsu tsana mara afuwa a kan kusan komai. Wannan na daga cikin dalilan da ke qazanta fadace-fadacen Musulmi da Kirista a yankin. Rayukansu na salwanta a sakamako.

Dattawansu ba sa tsinana mu su komai face daqile mu su damarmaki tare da sukarsu lailan wa naharan.

Malaman addininsu sun maidai malanta kasuwanci. Ba sa koyar da tsoron Allah sai raba kan al’umma.

Akasarin matasansu babu karatu sai daba da sata da zaman kashe wando (ga masu hankalin cikinsu).

‘Yan matansu sun tube wa kansu rigar kunya, sun koma zinace-zinace, da shaye-shayen qwayoyi.


Ƴa’yansu sun ƙware a zagi da ashar tare da nuna rashin kunya a gaban na gaba da su.

Shin ta ina za a samu kyakkyawan fata ga marainiyar al’umma irin wannan?

Muhammad Ibn Ibrahim

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan