Mutane Miliyan 20 Ne Su Ke Cikin Damuwa A Faɗin Najeriya – Farfesa Sani Malumfashi

445

Kimanin mutum miliyan ashirin ne ke fama da damuwa a fadin tarayyar Najeriya a shekaru uku da suka wuce.


Masanin halayyar dan Adam Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da shirin Barka da Hansti na Freedom Radio, da ke birnin Kano.

Farfesa Malumfashi yace sakamakon wasu al’amura na rayuwa da suka yi wa ‘’yan Najeriya tsamari shi yasa suke aikata wasu abubuwan da basu kamata ba ciki har da kashe kai ko kisan wani.

Shehin Malamin na jamiar ta Bayero ya kara da cewa kwayar halittar wasu ce ta saka suke aikata wasu daga cikin munanan halaye kamar kisan kai tun sanda aka haife su.


Yace kwayar halittar wasu mutanan tana da zafi wasu kuma tana da sanyi.

Fafesa Sani lawan ya kara da cewa ko aure mutum zai yi idan yana da zazzafan hali to kamata yayi ya auri mai sanyin hali idan kuma mace na da zafin hali to kamata yayi ta auri mai sanyin hali.


A nasa bangaren Kyaftin Abdullahi Adamu mai ritaya yace idan har bangaren Shariah zai tsayin daka wajen aiwatar da shari’u yadda suka kamata to shakka babu za’a samu raguwar kisan maza da mata ke yi ko kuma kisan mata da maza ke yi.

Freedom Radio, Kano

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan