Wani Mutum Ya Tallata Kansa A Allon Talla Domin Samun Masoyiya

41

Wani matashi da ke neman dacewa da samun masoyiyya ya sayi allon talla da ake dasawa a bakin titi inda aka lika hotonsa yana neman samun mai sonsa.

Mark Rofe wanda ya gaji da yadda manhajojin kulla alakar soyayya na zamani ke tafiyar da harkokinsu, ya yanke shawarar biyan £425 domin a sanya hotonsa a wani katon allo a bakin titi da ke Manchester.

Mark mai shekara 30 daga Sheffield yana fatan dacewa da masoyiyar da ta dace da shi.

Ya ce: “Na samu sama da mutum 1,000 da suka tuntube ni. Rabin wadanda suka tuntube ni maza ne amma ina jin dadi.”

Mr Rofe wanda ya shafe shekara guda ba tare da budurwa ba, ya ce ya sayi makeken allon mai fadin mita shida da tsawon mita uku domin yin zarra.

Ya ce “ina magana da wani abokina kan yadda nake shan wahala wajen samun budurwa ta manhajojin dalilin aure, inda da wasa na ce zan sa hotona a katon allon talla.

“Muka yi dariya amma daga baya sai na fara tunanin abu ne mai kyau.”

Katon allon wanda ke kan titin Fairfield Street ya nuna hoton Mark inda a kasan hoton aka sa adireshin shafinsa na intanet DatingMark.co.uk.”

Shafin na kunshe da tarihinsa inda ya bayyana kansa a matsayin “kyakkyawa kuma mai da’a” sannan yana maraba da duk wadda take da sha’awar kulla alakar soyayya da shi”

A sashen bayyana bayanai, ya ce shi mutum ne mai tsayi sannan dan yatsansa ya kai tsawon santimita 6.82 sannan ya taba sumbatar sama da ‘yan mata uku.

Mr Rofe ya ce ya yi matukar mamaki kan yadda mutane suka rika tuntubarsa kuma yana fatan amsa sakonnin wadanda suka turo masa sako.

Ya ce “wasu mutanen za su iya tunanin ni mahaukaci ne da har zan biya fam 425 amma idan na dace da masoyiya, to kudin bai yi wani tsada ba.

“Na yi kokarin yin abun cikin raha kuma ina fatan ba zan yi rashin nasara ba.”

BBC Hausa

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan