Ƴan Siyasa Ko Malaman Addini, Su Waye Ke Raba Kan Al’umma?

44

Wasunmu sukan ji dadin dora wa ‘yan siyasa alhakin raba kan al’umma ba tare da kallon lamarin daga ciki-ciki ba. Fikirar da suke yayatawa ita ce, wai ‘yan siyasa ke raba kan mutane ta fuskoki da dama.

Don haka da zarar wani abu ya faru sai su ce ai makircin ‘yan siyasa ne. Da haka sai ‘yan siyasanmu suka qara baqin jini a zukatan ayyuhan naasunmu.

Alhali a haqiqanin lamari, babu wadanda suka kai malaman addini, kama daga Kiristanci da dariqoqinsa zuwa Musulinci da mazhabobinsa, wargaza kan jama’a.

Malaman addini su ne qololuwa wurin fusta jama’a da raba kansu tare da ingiza su ga kashe-kashe a kan bambancin fahimta. Rabuwar kai ba aba ce da dan siyasa zai so ba, saboda za ta daqile masa quri’a.

Haka abin yake ga rikici ko fadace-fadace, don sukan kai ga haddin dora wa jiha ko qasa dokar ta-baci, abin zai iya hana zabe, kuma ya hana kudin shiga. Malaman addini ke amfana da hakan, saboda ba su da hasarar komai, kuma shugabancinsu na dindindin ne.

Mai buqatar hujja ga yadda Malamai ke haddasa rabuwar kan jama’a ya riqa ziyartar masallatai da majami’u na kowane bangare. Zai ji kalamai na tunzirarwa da nuna wariya a kan ‘yar sabanin da ba ta taka kara ta karya ba.

Dabarar malaman ga haka ita ce riqe mabiya. Idan suka firgita mabiyansu daga sauraran wasunsu, suna ganin ta hakan ne mabiyan za su yi riqo da su zalla har kuma alherai su yi ta gangarawa gare su.
Ba sa ganin cewa idan hakan ya auku, mabiyi yana wuce makadi da rawa ne. Domin tsanar da aka saqala masa ga wasunsa, takan kai shi ga hatta kisa.

A bincika dukkan tarihin fadace-fadacen addini da aqida a qasar nan, za a ga cewa malaman addini ke haddasawa ba ‘yan siyasa ba.

Allah ya raba mu da ulama’us suu’i.

Muhammad Bin Ibrahim, ya rubuto daga Kaduna

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan