Mai unguwar Danbare (D) dake karamar hukumar Kumbotso a Kano, Saifullahi Abba Labaran, ya ce sun bijiro da dokar gwajin kwakwalwa ga dukkanin masoyan da suke shirin angoncewa a yankin.
Malam Saifullahi Abba Labaran ya bayyana hakan ne a ganawar su da manema labarai a birnin Kano.
Ya kuma ce ” sabon tsarin wanda mahunkunta a yankin sun amince da shi, ya biyo bayan yawaitar samun kashe-kashen da ake yi a tsakanin ma’aurata, da nufin magance matsalar tun daga tushe. Domin kuwa mun shirya tsaf da wannan doka’’.

Ya kuma ce ” Zamu dauki mataki ga duk wani limamin da muka samu ya daura aure ba tare da ya tabbatar da shedar kwakwalwar masu shirin yin aure, sai mun gurfanar da shi a gaban mahukunta domin girbar abun da suka shuka”. inji Mai unguwa saifullahi.

A ƙarshe mai unguwar ya kuma shawarci sauran masu unguwanni da su zauna da sauran mahukunta dama al’umma a yankunan su daban-daban domin samar da irin wannan doka ta cikin gida.
Dala FM Kano