Liverpool ta Shirya Tsawaita kwantaragin

81

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila kuma zakarun gasar nahiyar turai ta shirya tsawaita kwantaragin dan wasanta mai tsaron baya wato Van Dijk.

Wannan tsawaita kwantaragi ya biyo bayan daka wawa da kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Italia take neman yiwa dan wasan.

Juventus dai ta bayyana cewar ko nawa ne zata iya sakawa ta sayi wannan dan wasa.

Ganin kada ayiwa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool sakiyar da babu ruwa shine suka bayyana cewar sufa kara tsawaita kwantaraginsa zasuyi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan