Masarautar Ƙaraye Na Da Rubutaccen Tarihi Fiye Da Shekaru 900 – Sarkin Ƙaraye

8

Mai martaba Sarkin Ƙaraye Dakta Ibrahim Abubakar II yace masarautar Ƙaraye tana da rubutaccen tarihin masarautar na tsawon shekaru ɗari 900.

Sarkin na Ƙaraye ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar manyan jami’ai ƙarkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido na jihar kano Alhaji Ibrahim Ahmed Karaye a fadarsa.

A nasa ɓagaren kwamishinan ma’aikatar raya al’adu yawon buɗe ido, Alhaji Ibrahim Ahmed Karaye ya bayyana cewa gwammatin jihar Kano a yanzu haka ta fara shirye shiryen amso kayayyakin tarihi mallakin jihar Kano waɗanda tsawon shekaru su ke can a ajiye a gidan tunawa da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto (AREWA HOUSE KADUNA)

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan