Yau Ake Bikin Ranar Yaki Da Ciwon Daji Ta Duniya

158

Ranar 4 ga watan Fabrairu ake tarukan ranar ciwon daji ta duniya, cutar da ke kama mutane miliyan 14 kowacce shekara.

Manufar dai ita ce, karawa jama’a fahimta dangane da cutar ta Cancer da kuma kawar da duk wasu tunani dake da nasaba da al’ada dangane da wannan cuta mai hallaka jama’a.


Hukumar lafiya ta duniya, wato WHO ta ce, cutar ta Cancer ce kan gaba wajen hallaka jama’a a duniya, kuma ta ce, koda a shekara ta 2008 cutar ta hallaka mutane fiye da miliyan bakwai.


A ƙasashen Afurka wannan cuta ta Daji na hallaka jama’a da dama saboda dalilai da dama da suka hada da rashin gano ta akan lokaci da kuma rashin kayan aiki a asibitoci domin kula da masu fama da cutar da kuma tunani iri iri masu nasaba da al’ada dangane da wannan cuta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan