An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kano

136

A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tsige Shugabanta Masu Rinjaye, Labaran Abdul-Madari ta maye gurbin sa da mataimakinsa, Kabiru Hassan-Dashi.

Majiyarmu ta bada rahoton cewa tsige Shugaban Masu Rinjayen ya zo ne jim kaɗan bayan wani ƙuduri na gaggawa da sabon ɗan majalisar jam’iyyar APC mai wakiltar Mazaɓar Bunkure, Muhammad Uba-Gurjiya ya gabatar.

A jiya Talata ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kanon, Abdul’azeez Garba-Gafasa ya rantsar da Mista Uba-Gurjiya bayan nasarar da ya samu a zaɓen cike gurbi da aka yi kwanan nan.

A ta bakin Mista Garba-Gafasa, an ɗauki matakin tsige Shugaban Masu Rinjayen ne biyo bayan amincewar ‘yan majalisar APC 23 daga cikin su 28, daga cikin mambobi 40 da Majalisar Dokokin Jihar Kanon ke da su.

Nan da nan wani ɗan majalisar APC mai wakiltar Mazaɓar Ɓagwai/Shanono, Ali Ibrahim-Shanono ya goyi bayan ƙudirin.

Majiyarmu ta ce bayan zartar da ƙudirin, sai ‘yan majalisar suka buƙaci Shugaban Masu Rinjayen da ya sauka.

Bayan tsige Shugaban Masu Rinjayen, sai wani ɗan majalisar jam’iyyar APC, Hamza Missau, mai wakiltar Mazaɓar Sumaila ya bada sunan Mataimakin Shugaban Masu Rinjayen, Kabiru Hassan-Dashi don zaɓar sa a matsayin Shugaban Masu Rinjayen.

Wasu mambobin majalisar sun amince da bada sunan, majalisar ma ta amince, hakan ne yasa Mista Hassan-Dashi ya zama Shugaban Masu Rinjaye nan take.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan