Lai Mohammed wanda shi ne Ministan yada labarai da al’adu ya ce babu ta inda kudirorin daidaita kafafen sada zumunta taci karo da hakkin da doka ta yi wa ‘Yan Najeriya tanadi.
Duk da rashin tsaron da ake fama da shi a yanzu, Ministan ya fito gaban Duniya ya na bayyana cewa Najeriya ce kasar da ta fi kowace aminci a kaf Duniya.
Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan kasar Finland a Najeriya, Dakta Jyrki Pulkkimen inji Jaridar nan ta Pulse.ng.
Dakta Jyrki Pulkkimen da Tawagarsa sun kawowa Ministan tarayyar ziyara ta musamman ne a ofishinsa da ke Abuja a Ranar Litinin, 3 ga Watan Fubrairun 2020.
A dalilin wannan zama da Jakadan Finland ne har gwamnatin Najeriya ta fara shirin kiran taro na masu ruwa da tsaki wajen sha’anin dandalin yada zumunta.
Kudirorin da ke gaban majalisar tarayya za su kawo gyara ne a shafun sada zumunta, sannan kuma su kawar da yada kalaman batanci, a cewar Ministan kasar.
