Wata Mata Ta Haifi Zankaɗeɗiyar Jaririya A Cikin Motar Haya

298

A ranar Litinin din nan da ta gabata ne wata mata mai suna Nkechi Okechukwu, ta haifi jaririyarta ta biyu a cikin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa asibiti tare da mijinta, Okechukwu.

Matar ta wallafa labarin na ta a shafinta na Instagram, inda ta bayyana dalla-dalla yadda ta haifi jaririyar ita daya a cikin mota tare da mijinta da kuma direba wanda ya cika da fargaba.

“Ban tabbatar da cewa nakuda ba ce sai da safiyar yau da misalin karfe 6:30 na safe. Duk da yake dai ba wani ciwo nake mai tsanani ba amman dole muka tafi asibiti da misalin karfe 6:50 na safe. Mun je asibitin Eko Ikeja daga Ogba. Kasancewar masu bada hannun gurin barayi ne. Mun yanke shawarar mu kama hanyar Oregun.

“A lokacin ciwon ya na ta kara tsananta tare da radadi marar misali. Amma dai kawai na ci gaba da gaya wa kaina cewa zamu je asibitin cikin lokaci kamar yadda ruwana bai fashe ba a lokacin. Kwatsam sai ji nayi ruwana ya fashe, hakan ya faru da misalin karfe 7:30 ko makamancin haka. Kuma cikin nutsuwa na sanarwar da mijina dake zaune a gaba kusa da direba.

“A wannan lokacin ne na dinga tinawa da gargadin da ake yiwa mata akan yawan motsa jiki. Haka nayi ta faman kokari da nishi cikin wahalar nakuda ina kokarin fito da jaririyar, yayin da shi kuma mijina yake kokarin taimaka mini ta hanyar duk yin duk wani abu da yaga ya dace“

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan