Al’ummar unguwar Gayawa da ke yankin ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano suna zama cikin fargabar ambaliyar ruwa masamman idan damuna ta sauka.

Sakamakon zaizayar ƙasa da ke ƙoƙarin cinye unguwar, wanda hakan babbar barazana ce ga mazauna wannan unguwa.

Masana binciken yanayi sun tabbatar da cewa Hamada na barazana ga kasar nan da kashi 6 a duk shekara, haka zalika ana asarar sama da kadada dubu uku na filayen noma sakamakon zaizayar kasa.


Matsalar zaizayar kasa babbar matsalace da ke addabar wasu yankuna na jihar Kano, domin ko a cikin watan Mayun shekarar 2019, a kokarin da ta ke na kawo karshen matsalar zaizayar kasa, Gwamnatin Jihar Kano ta biya Naira Miliyon 500 shirin hadin guiwa da gwamnatin tarayya domin magance matalar tare da hukumar (NEWMAP).