An Kama Mawaƙin Kwankwasiyya Da Yayi Waƙar Nan Mai Taken ‘A Wanki Gara’

16

Jami’an tsaro a jihar Kano sun ka kama wani mawakin siyasa da ke jihar Katsina mai suna Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da ‘Kosan Waka’.

Kamar yadda mujallar Hausa ta Fim Magazine ta ruwaito, matashin mawakin dan a mutun kungiyar Kwankwasiyya haka kuma ya na daya daga cikin manyan mawakan Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Aminu Bello Masari.

Mawakin na yin waka da salon fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara.

Ana dai zargin kama shi din bai rasa nasaba da wata sabuwar waka da ya fitar a shekaranjiya mai taken ‘A Wanki Gara’.

Mujallar Fim Magazine ta nemi ta gano inda aka wuce da shi a Kano da kuma wanda ya kai shi kara har aka kama shi din, amma hakan ba ta samu ba.

Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan an bayyana cewa an kulle kamfanin fitaccen jarumin nan na masana’antar Kannywood wato Sani Danja.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan