Hukumar INEC Ta Soke Rijistar Jam’iyyu 74

134

Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta, INEC ta soke rajistar jam’iyyun siyasar kasar nan guda 74, abin da ke nufin cewa, jam’iyyu 18 kacal suka tsallake shirinta na rage yawan jam’iyyu a faɗin kasar nan.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar ta INEC ta yi nazari tare da tantance rawar da jam’iyyun siyasar suka taka bayan kammala zabukan 2019 , inda ta gano jam’iyyun da suka cancanci ci gaba da wanzuwa.

Wannan mataki da hukumar ta INEC ta ɗauka ya kawo ƙarshen jam’iyyar PRP, wacce ko a cikin shekarar zaɓe ta 2019 sai da Malam Salihu Sagir Takai, ya yi takarar neman gwamnan jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan