Jaruma Halima Atete Ta Yi Rashin Mahaifiyarta

16

Fitacciyar jarumar fina-finan Kanywood Halima Atete ta yi rashin mahaifiyarta a yau Alhamis.

Cikin wata sanarwa da shafin Kanywood Movies ya wallafa, sanarwa ta kara da cewa za a yi jana’izar Mahaifiyar ta Halima Atete a babban masallacin kasa da ke Abuja.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Allah yayiwa mahaifiyar Jaruma Halima Atete Rasuwa a safiyar yau a asibiti a Abuja bayan doguwar jinya da tasha Allah yasa mutuwa hutuce agareta Amin mukuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani. -@usmanmuazu20”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan