Musulmai Sun Buɗe Asibitin Da Ake Duba Lafiyar Talakawa Kyauta A Ƙasar Amurka

107

A kokarinsu na ganin sun taimakawa marasa karfi da galihu, wata kungiyar likitoci Musulmai a Toledo dake jihar Ohio sun bude asibiti kyauta domin bayar da magani kyauta ga duka talakawan wannan gari, kamar yadda jaridar Teoledo Blade ta ruwaito.

“Mun gabatar da taro, sai muka ga ya kamata mu samo wata hanya da zamu taimakawa mutanen garinmu, kawai sai muka yanke shawarar bude wannan asibiti kyauta,” cewar Dakta Sulaiman Abawi, daya daga cikin likitocin cibiyar lafiya ta Fulton County.

“Dukkan mu muna son ganin mun taimakawa mun bawa talakawa abinda ba su dashi, mun dai tunanin iya kan mu da iyalanmu kawai,” ya kara cewa.

Lokacin da yake basu da takamaiman waje, sai suka fara zuwa unguwannin mutanen da basu da karfi suna basu magani, daga nan kuma sai suka bude dan karamin dakin bayar da magani a Masallacin Al-Islam dake yankin arewacin Toledo.

Daga baya wani babban likita, Dakta Mahmood Moosa ya bayar da fili kyauta aka bude asibitin Halim.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da likitoci Musulmai suka bude cibiyoyin bada magani ba ga talakawan kasar Amurka. A watan Afrilun shekarar 2018, Musulmai a yankin arewa maso gabashin Philadelphia sun bude cibiyar bayar da magani kyauta ga talakawan yankin.

Haka a yankin kudancin Carolina, nan ma an bude asibitin Shifa wanda yake bayar da magani ga talakawa a wannan yankin.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan