Pantami Ya Haramta Amfani Da Layukan Waya Fiye Da 3

164

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Dakta Isa Ali-Pantami ya umarci Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Ƙasa, NCC, da ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya ba sa yin amfani da layukan waya da suka haura uku.

Ministan ya bada umarnin ne ranar Laraba a cikin wata sanarwa da Ƙwararren Mataiamkinsa, Dakta Femi Adeluyi ya sanya wa hannu, yana mai umartar NCC da ta sake duba tsarin yadda yi wa layukan waya rijista da kuma yadda ake amfani da layukan.

Sanarwar ta kuma lura da cewa sake duba tsarin yin rijistar layukan ya biyo bayanai da aka samu daga hukumomin tsaro biyo bayan nasarar da aka samu wajen sabunta rijistar layukan da ba a yi musu rijista daidai ba, da kuma toshe layukan waɗanda suka ƙi sabunta rijistar layukan nasu.

Ministan ya kuma umarci NCC da ta tabbatar da ana amfani da Lambar Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIN a wajen yi wa ‘yan Najeriya rijistar sabbin layuka, ‘yan ƙasashen waje kuma za a yi amfani da fasfot da bizarsu wajen yi musu rijistar layukan.

A ta bakin Mista Ali-Pantami, kafin 1 ga Disamba, 2020, za a sabunta layukan dake da Rijistar a halin yanzu da NIN.

“Ta tabbatar da cewa wakilai masu cikakkiyar tantancewa ne kaɗai suke tallafa wa tsarin rijistar, ba tare da su ma suna yin amfani da layuka marasa rijista ba, yayinda kamfanonin sadarwa za su aiwatar da rijistar;

“Dole a taƙaita layuka da mutum ɗaya zai iya amfani da su, wata ƙila 3;

“Ta tabbatar da cewa ba a bar layuka marasa rijista suna aiki a rumbunan sadarwa ba;

“Ta tabbatar da cewa masu amfani da layuka za su iya duba adadin layuka da aka yi wa rijista da sunayensu da lambobin waya da kamfanonin sadarwar;

“Ta tabbatar da cewa kamfanonin sadarwa suna kare na’urorinsu daga hare-haren ɓarayin Intanet, kuma ta tabbatar suna bin tanade-tanaden Nigeria Data Protection Regulation, NDPR; da

“Ta tabbatar da cewa an toshe layukan da aka yi amfani da su wajen aikata laifuka har a abada”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan