Wasu Da Ake Zargin Ƴan Fashi Da Makami Ne Sun Harbe Wani Matashi A Kano

132

Wasu ‘yan fashi da makami da ba a iya gane su ba dauke da bindigogi a na zargin sun shiga gidan wani mutum mai suna Alh. Munir Na’iya a unguwar Hotoron Maradi dake karamar hukumar Tarauni.

Ƴan fashin sun karbe masa tarin kudi masu yawa a cikin jaka kafin daga bisani su ka tafi suna harbe-harbe a iska a yammacin ranar Laraba.

A zantawarsa da manema labarai Munir ya ce,
“Ina kwance na ji su na buga min gidana, sun tadda mata a daya gidan, na za gaya na fita sai su ka shigo da ni, su na harbe-harbe, su kace kudi na ce to, kafin ma na hau sama wani ya shiga su ka ta harbe-harbe su ka fita”.

Ita kuwa ‘yar mai gidan Fatima Munir ta ce, “Mu na zaune sai na ga baban mu ya fito da sauri, fitowar da za mu yi bakin kofa sai na ga sun rike baban mu, sai na ce mai za ku yi wa baban mu, me ya yi muku? Sai babar mu ta riko wuyanta sai ya sakar ma ta bindiga, ni kuma ganin ya sakar ma ta bindiga sai na riko wuyan dayan, sai ya kifa min mari”.


Bayan ‘yan fashin sun fito daga gidan ne su ka fara harbe-harbe wanda sanadiyar hakan ne a ka yi zargin sun harbe makocin Alhajin, mai suna Ali Usman har lahira kamar yadda abokin sa da su ke tare a lokacin ya shaidawa manema labarai

“Mu na dakina mu na kallo da wanda ya rasu, sai wani abokina ya shigo ya ce unguwar nan babu lafiya ya ce ya ga wasu mutane sun yi sallama da makocin mu su na harbe-harbe sun shiga gidan, mun fito bayan sun wuce sai mu ka ga an harbi abokin namu”. Inji abokin marigayin.


Kazalika mun tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bakin Kakakin ta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce, za su bincika al’amarin.

Dala FM Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan