‘Yan Najeriya Miliyan 25 Ke Fama Da Larurar Nakasa- Fadar Shugaban Ƙasa

38

Dakta Samuel Ankeli, Mataiamki Na Musamman Ga Shugaba Muhammadu Buhari Kan Mutane Masu Larurar Nakasa ya ce ‘yan Najeriya miliyan 25 na rayuwa da larurar nakasa.

Mista Ankeli ya bayyana haka ne ranar Alhamis yayinda yake jawabi ga ɗaliba masu larurar nakasa na Jami’ar Ilorin a yayin wani shiri irinsa na farko da ɗaliban suka shirya mai taken: “Ability in Disability”.

Mataimakin na Shugaban Ƙasa ya yi alƙawarin taimaka wa jami’ar wajen samar da matsuguni da cibiyoyi na musamman don amfanin ɗalibai masu larurar nakasa.

A wani jawabi da mutane da dama suka kalla a matsayin “mai zaburarwa”, Mista Ankeli, wanda kuturu ne, ya ce Shugaban Ƙasa yana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa an kare haƙƙoƙin mutane masu larurar nakasa.

Ya ce Shugaba Buhari ya damu da “Dokar Mutane Masu Larurar Nakasa”, wadda ya ce za ta tabbatar da adalci da daidaito ga mutane masu larurar nakasa a ƙasar nan.

A cewarsa, buƙatar Shugaba Buhari ita ce ya ga masu larurar nakasa sun samu wakilci, kuma su zama daga cikin ɓangaren zamantakewa da siyasa.

A cewar Mista Ankelu, dukkan mutane an haife su ne daidai, ya kuma kira ga ɗaliban da su yi amfani da abubuwan da za su iya yi duk da ƙalubale.

Mista Ankeli ya roƙi ‘yan Najeriya da su riƙa tallafa wa mutane masu larurar nakasa maimakon tausaya musu..
Ya yi kira gare su da su yi aiki tuƙuru, yana mai cewa hakan zai haifar musu da abin alheri.

Mataimakin ya jaddada muhimmancin samun Mai Bada Shawara Kan Mutane Masu Larurar Nakasa a gwamnatin jihar Kwara don tafiyar da al’amuran masu larurar ta nakasa yadda ya kamata.

Da yake jawabin maraba tunda farko, Farfesa Sulyman Abdulkareem, Shugaban Jami’ar, ya ce jami’ar tana ƙoƙari ƙwarai da gaske don ganin ɗalibai masu larurar nakasa sun iya amfani da kayyakin karatu.

Mista Abdulkareem, wanda ya samu wakilcin Farfesa Olayinka Buhari, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Bincike da Sabbin Abubuwa, ya bayyana cewa hukumar gudanarwar jami’ar ta tabbatar da cewa ɗaliban jami’ar masu larurar nakasa dake nazarin Shari’a an ba su kulawa ta musamman.

Ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su tabbatar da samun damammakin samun aiki ga ɗaliban bayan kammala karatunsu.

Dakta Payricia Atejere, Muƙaddashiyar Daraktan wata cibiyar jami’ar mai suna “Centre for Supportive Services for the Deaf, CSSD”, ta nuna rashin jin daɗi bisa yadda mutane ke fahimtar larurar nakasa.

Ta nuna ɓacin rai kan yadda ake nuna wa mutane masu larurar nakasa bambanci.

“Dole cikin tsari mu rushe irin tausayin da ƙwaƙwalwarmu take sa muna ba mutane masu buƙata ta musamman.
“Tausayawa tana nesanta mutum mai larurar nakasa daga jama’a, tana hana su damar neman ilimi, aikin yi sannan tana hana su cimma burinsu”, in ji ta.

Ta bayyana cewa tun daga lokacin da aka kafa wannan cibiya, ta yaye ɗalibai makafi 65 daga sassa daban-daban na jami’ar.

Wisdom Oluwaseun, Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ta Jami’ar, SUG, ya yi kira ga ɗalibai masu larurar nakasa da kada su karaya, amma su yi amfani da “iyawa a cikin nakasa”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan