Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Jami’ar Musulunci Ta IUIU

202

Jami’ar Addinin Musulunci da ke ƙasar Uganda, wato Islamic University In Uganda (IUIU), Jami’a ce wacce aka kafata kimanin shekaru 32 da su ka wuce.

Wannan Jami’a Ta Fara da dalibai guda 80 da kuma fannin digiri guda biyu, amma saboda irin nagarta da amincin ilimin da wannan jami’a ta ke bayarwa, yau wannan Jami’a tana Ɗalibai sama da 10,000 daga sassa daban-daban na faɗin duniya.

Jami’ar IUIU tana da Tsangayoyi wato Faculties guda 7, sai kuma sashe-sashe wato Departments fiye da guda 70. Wanna ce ta sanya Jami’ar Ke Alfahari da dimbin Daliban da ta yaye akan fanni daban-daban. Domin ƙididdiga ta nuna cewa wannan jami’a ta yaye dalibai fiye da 25,000, wanda yanzu haka suna aiki a gwamnatocin ƙasashe, manyan masana’antu, kafafen yaɗa labarai, asibitoci da kuma jami’o’i.

A ɗaya ɓangaren kuma wannan jami’a ta IUIU tana da ɓangaren karatun digirin digirgir wato School of Postgraduate Studies. wanda ake karatun digiri na biyu wato Masters da kuma digiri na uku wato PhD.

A ɓangaren malamai kuwa wannan jami’a ta IUIU tana da ƙwararrun malamai, masana fiye da guda 600, waɗanda sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya.

A ɓangaren koyarwa kuwa, Jami’ar IUIU tana da ƙwararun malaman da ke bayar da ingantaccen ilimin da duniya ke tinƙaho da shi, haka kuma a harkar na’ura mai ƙwaƙwalwa da fasahar sadarwa, Jami’ar IUIU ta yi fice a cikin jerin takwarorinta.

Hakazalika, Jami’ar IUIU tana bin tsarin Shari’ar Musulunci, la’akari da yadda ta keɓe ɓangaren mata ɓangare guda.

Tsangayoyin Wannan Jami’a Ta IUIU Wato Faculties

Jami’ar IUIU tana da Tsangayoyin karatu wato Faculties guda 7 da su ke bayar da Digiri fiye da guda hamsin, waɗanda su ka haɗa da:

  1. Tsangayar Addinin Musulunci Da Kuma Harshen Larabaci. Wato Faculty of Islamic Studies and Arabic Language
  2. Tsangayar Fasaha Da Zamantakewa Wato Faculty of Arts and Social Sciences
  3. Tsangayar Harkokin Gudanarwa
    Faculty of Management Studies
  4. Tsangayar Ilimi Wato Faculty of Education
  5. Tsangayar Kimiyya Wato Faculty of Science
  6. Tsangayar Koyon Aikin Lauya Wato Faculty of Law
  7. Tsangayar Koyon Aikin Kiwon Lafiya Wato Faculty of Health Sciences.

Wannan Jami’a ta yi fice akan ɓangaren aikin Likita wato Medicine, Kimiyyar hada Magunguna wato Pharmacy, Aikin Lauya wato Law, Aikin Jarida Wato Mass Communication, Harkokin Kasuwanci Wato Business Administration, Na’ura mai kwakwalwa wato Computer Science, Fasahar Sadarwa Wato Information Technology, Aikin Jinya da Unguwar Zoma Wato Nursing And Midwifery da sauran Kwasa-kwasai da duniya ta ke muradinsu.

A cikin Shekarar 2019 hukumar kula da jami’o’i masu zaman kansu ta ƙasar Uganda ta bayyana Islamic University In Uganda (IUIU), a matsayin Jami’a ta farko a jerin jami’o’in kasar wato Best Private Institution In The Country.

Waye Ya Cancanta Ya Samu Gurbin Karatu A Jami’ar IUIU Kampala?

Duk Dalibin Da Ya Ke Da Credits Guda 5, Ciki Ya Kasance Akwai Turanci Da Lissafi wato Five Credits Including Mathematics and English, to babu shakka zai samu Gurbin Karatu a wannan mashahuriyar Jami’a.

Haka kuma akwai bangaren Remedial ga wadanda su ke da matsala a takardun sakandirensu wato Remedial Section.

Yaya Ake Samun Gurbi A Wannan Jami’a Ta IUIU?

Ana Samun Shiga Wannan Jami’a Ne Ta Hanyar Siyan Fom Wato IUIU Entry Form Akan Kudi Naira 10,000 a matakin Karatun Digiri, Sai Kuma Naira 15,000 A Matakin Karatun Digiri Na Biyu Da Na Uku.

Domin Karin Bayani za a iya tuntubarmu ta wannan Lamba (Both Call and WhatsApp) domin samun gurbin karatu a wannan Mashahuriyar Jami’a Ta IUIU
+256783738159
+256757565884
abusamiharano@gmail.com

Ko kuma kai tsaye a office din su da ke Dan Amarya Plaza, Maiduguri Road, Tarauni, Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan