Ba Zan Goyi Bayan Buhari Ba Idan Zai Yi Ta-zarce — Santa Shekarau

151

Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce ba zai goyi bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba idan ya nemi karin wa’adi karo a uku.


Shugaba Buhari dai ya sha musanta zargin da wasu ‘yan kasar, musamman ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP, ke yi cewa yana so a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin ya ci gaba da mulki kar na uku.


Sai dai a tattaunawarsa da BBC kan kudurin da majalisar dattawan kasar ta amince da shi na bukatar gyaa ga kundin tsarin mulkin kasar, Sanaa Shekarau ya ce ba ya tsammanin Shugaba Buhari zai nemi yin ta-zarce saboda kaunarsa ga mulkin dimokradiyya.


“Ni dai a iya sanina ban san asalin wannan magana [yunkurin ta-zarcen Buhari] ba; idan ma akwai ta ni ban ji ta ba, ba a yi da ni ba…ko da irin wannan batu zai zo ina daga cikin sahun gaba da za su ce basu yarda ba.”

Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci ‘yan kasar su kyautatawa Shugaba Buhari zato, yana mai cewa “yadda nake kyautata wa Janar Buhari zato ko da mafi kusancinsa sun kawo masa irin wannan tunani, ga hange na ba najin zai karbi wannan tsaro.”


A cewarsa, idan Buhari ya nemi yin ta-zarce hakan zai haifar da fitina a kasar.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan