Da Kuɗin Alawus Ɗin Da Ake Bani Na Sayi Babur Ɗin Adaidaita Sahu – Ƴar Bautar Ƙasa

312

Wata matashiya mai suna Uwaoma Susan Joseph dake yi wa kasa hidima bayan ta kammala karatun ta na Jami’a ta sayi babur mai kafa uku da aka fi sani da (Keke-Napep) da kudin da take tarawa na Alawus da gwamnatin tarayya ke biyanta a duk karshen wata.

Matashiyar ta bayyana a shifinta na Facebook, inda ta bayyana cewa nan da wasu ‘yan kwanaki za ta gama aikin hidimar kasa da take yi, kuma da ɗan abin da ake bata a matsayin alawus ta sayi wannan Keke-Napep.

A cewar ta, “gwamnatin tarayya na biya na naira dubu 19,800 a kowani wata sannan inda nake aikin hidimta wa kasa na biya na naira dubu 20,000 a duk karshen wata, kudin nake tarawa sai a karshen watan jiya na duba ya kai ga naira dubu N432,000”.

Uwaoma ta ce da kudin ne ta sayi wannan Keke-Napep din duk da cewa ba sabo bame kuma ta ba ma wani ya na yi mata jigila da shi, kuma ta bayyana cewa ta na samun taro sisi a kowani wuni.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan