Ganduje Ya Bada Kyautar N500,000 Ga Mutumin Da Ya Yi Tattaki Daga Katsina Zuwa Kano Don Taya Shi Murnar Nasara A Kotu

136

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Kwamared Nura Aliyu Batsari goma ta arziƙi, mutumin da ya tattaki daga jihar Katsina zuwa Kano don taya gwamnan murnar samun nasara a Kotun Ƙoli.

A cewar jaridar Katsina Post, Gwamna Ganduje ya ba Mista Aliyu-Batsari kyautar N500,000, kujerar aikin Haji da sabuwar kwamfuta.

A cewar Katsina Post, dama tun kafin wannan kyauta, Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila ya ba wannan mutumi da ya tattaki sarautar ‘Sarkin Zumuncin Rano’ lokacin da ya kai masa ziyara a fadarsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan