Tarihi: Shekaru Biyar Da Baiwa Sarkin Kano Sanusi II Sandar Mulki

82

Ranar 7 ga watan 2 na shekarar 2015 tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya mika sandar mulki ga Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, a babban ɗakin taro na Coronation da ke gidan gwamnatin jihar Kano, kuma an gina wannan ɗakin taro domin girmama wannan rana ta tarihi.

A ranar 8 ga watan Yunin Shekarar 2015 ne aka nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar Sarki Ado Bayero a ranar 6 ga watan Yunin Shekarar.

Baki daga ciki da wajen ƙassr nan ne suka hallarci taron wadanda suka hada da Jakadan Amurka a Najeriya, Mr. James Entwistle da tsofaffin shuwagabannin ƙasar nan, kamar Janar Muhammadu Buhari, Yakubu Gowon da Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, da sauran sarakuna daga arewaci da kudancin ƙasar nan.

Bikin bayar da sandar mulkin dai shi ne karo na farko da aka bayar da sanda ga sarki a masarautar Kano tun shekarar 1963.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan