Abduljabbar Surajo Guga; Matashin Attajiri Mai Zuciyar Alkhairi

227

Asali Da Tarihin Karatun Abduljabbar Surajo Guga

Abduljabbar Surajo Guga matashi ne dan kabilar Hausa fulani da ya fito daga garin Guga a yankin karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.

Masu iya magana kan ce Hanya bata barin gida, wannan gaskiya ne, domin Abduljabbar Guga ya yi gadon halin kwarai ne daga mahaifinsa, domin a bayyane take mahaifinsa, dattijo ne mai hallin dattaku.

Kamar yadda ya ke a tarbiyyar ƙasar Hausa, wacce tarbiyya ce da aka cuɗanyata da addinin islama, Abduljabbar Surajo ya fara karatunsa na addinin Islama a Islamiyyar Malam Baba da kuma Islamiyyar Malam Yahaya.

Abduljabbar Guga ya samu nasarar shiga makarantar Primary din Sarki Nursery School Yarmouk da kuma babbar sakandiren Kaduna Kapital.

Bayan kammala karatun Sakandire, a cikin Shekarar 2007 ne Abduljabbar Guga ya samu nasarar tafiya ƙasar Amurka, domin zurfafa iliminsa akan fasahar sadarwa a babbar kwalejin Lowa, wato Lowa Central Community College, daga nan kuma ya wuce mashahuriyar Jami’ar nan ta Missouri Saints Louis (UMSL).

Abduljabba Guga mutum ne mai hazaƙa da kuma kaifin basira, wanda hakan ne ya bashi damar samun aiki a lokacin da ya ke Karatu a ƙasar ta Amurka.

Aiyuka Da Gwagwarmayar Abduljabbar Surajo Guga

Ya samu nasarar fara aiki a babban kamfanin na Triggerfish Corporation Information Technology da ke ƙasar Amurka, a cikin shekarar 2017. Ya kuma zama Babban manaja akan fasahar sadarwa a kamfanin Northwest Health Service. Hakazalika, shi ne shugaban kamfanin Al Nur Tech LLC Computers St. Joseph da ke jihar Missouri, a ƙasar Amurka.

Taimakonsa Ga Al’umma

Haƙiƙa duk mai bibiyar harkokin al’amuran yau da kullum tare da kafafen yaɗa labarai to babu shakka sunan Abduljabbar Surajo Guga ba baƙon suna bane a gare shi. Domin shi ne shugaban babbar gidauniyar nan ta Guga Global Foundation da ke gudanar da aiyukanta ƙasar nan da kuma ƙasar Amurka.

Wannan Gidauniya ta Guga Global Foundation ta baiwa ɗimbin al’umma gudummawa ta ɓangarori mabambanta. Musamman ɓangaren taimakon Marayu, ta hanyar samar musu da ingantaccen Ilimi tare da baiwa iyayensu jari domin dogaro da kai.

Kamar yadda ya ke a bayyane, al’umma na fama da matsalar wanda zai tallafi rayuwar matasa musamman a harkar ilimi, wannan Gidauniya ta Guga Global Foundation da aka samar da ita da nufin ɗaukar nauyin karatun ɗalibai Marayu, a faɗin jihar Katsina.

Abin sha’awa da kuma kwaikwayo shi ne yadda wannan matashi ya mayar da hankalinsa wajen ganin al’ummar da ya fito daga cikinta ta samu ingantaccen Ilimi na zamani wanda duniya ta ke yayi.

Nasarorin Abduljabbar Surajo Guga

Jajircewa da kuma Sadaukarwa suna daga cikin sirrin samun nasara a rayuwa, Abduljabbar Surajo Guga ya samu dimbin nasararori a ciki da wajen kasar nan.

La’akari Da Yadda Ya Ke Taimakon Al’umma Da Kuma Taimakon Marayu babu dare babu rana, hakan ya sanya masarautar Daura a jihar Katsina, ta bashi Sarautar Garkuwan Matasan Hausa, a cikin shekarar 2019.

A har kullum addu’ar mu ita ce Allah ya azurta yankin arewacin ƙasar nan da irin waɗannan matasan masu abin hannu, wanda kuma su ke da zuciyar taimako, Amin.

Muhammad Buhari Abba, 08032649118 ya rubuto daga Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan