Alhakin Taɓarɓarewar Tsaro A Ƙasar Nan Ya Rataya A Wuyan Ƴan Siyasa Da Sarakuna – Sultan

154

Mai alafrma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya dora laifin matsalar tsaro akan manyan kasar nan da kuma ‘yan siyasa.

Ya ce: “Sun kasa jagorantar talakawa zuwa tudun mun tsira.”

Haka kuma Sultan ya kara dora laifin akan sarakunan gargajiya da malaman addini akan kasa rashin kokarinsu wajen dora mutane akan hanyar zaman lafiya da gaskiya, haka kuma ya kara da cewa rashin hankuri na ‘yan Najeriya shima ya kara sanya kasar cikin tashin hankali.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakane a jihar Filato, a lokacin da yaje taron tunawa da mutanen da rikicin jihar ya rutsa da su, wanda aka gabatar a jiya Juma’a a garin Jos babban birnin jihar.

Sultan ya ce: “Ina daukar irin wannan taro da matukar muhimmanci, saboda haka dole na bukaci gwamnan jihar nan ya koyawa mutane yadda ake hakuri da juna da kuma yafiya.”

Haka shima a nasa bangaren gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya bayyana cewa ana bukatar mutanen jihar da su yi hakuri da juna su zauna lafiya, su kuma manta da duk wasu banbance-banbance.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan