Ba Zan Iya Sasanta Ganduje Da Sarki Sanusi Ba- Buhari

110

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya bai ba shi dama ya tsoma baki a turka-turkar da ake yi tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Sarki Muhammad Sanusi II ba.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawunsa, Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamna Ganduje da sabbin ‘yan majalisar jihar Kano na jam’iyyar APC da aka zaɓa.

Shugaba Buhari ya ce: “Na san aikina a matsayin Shugaban Najeriya. Bisa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, gwamman jihar Kano yana da aikinsa, idan wata magana tana gaban Majalisar Dokokin Jiha (kamar Kano), Shugaban Ƙasa ba shi da iko ya sa baki.

“Ina aiki da Kundin Tsarin Mulki ne, na rantse da shi, kuma zan ci gaba da aiki da wannan rantsuwa. Amma bari in faɗa muku ƙololuwar fahimtata ita ce dole a tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga dukkan ‘yan Najeriya, inda ake yi wa mutane barazana, to a nan zan yi amfani da ikona da Kundin Tsarin Mulki ya ba ni”.

Shugaba Buhari ya shawarci sabbin ‘yan majalisar da su cika alƙawaran da suka yi wa al’ummarsu don sauke amanar da suka ɗauka.

“Ina fata kuna sane da alƙawuran da kuka yi wa mazaɓunku. Kun zagaya kuma kun yi wa mazaɓunku alƙawura. Ina fata alƙawuran da kuka yi sun yi daidai da tattalin arziƙin jiharku. Idan kuka yi alƙawuran da suka fi ƙarfin tattalin arziƙinku, zai zame muku matsala saboda za ku ƙara yin takara nan da shekaru huɗu masu zuwa. Wannan yana da muhimmanci kuma yana da muhimmanci ga jam’iyyarmu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan