Duk Lokacin Dana Bushi Iska Nima Zaku Ganni Tsirara – Nafisat Abdullahi

382

Masu bibiyar shafin fitacciyar jaruma Nafisat Abdullahi na Twitter sun fusata ta, inda ta yi wasu kalamai da suka sake jawo kace-nace a shafin nata.

Idan ba a manta ba a jiya ne bayan sakin bidiyon tsiraicin kawarta Maryam Booth a shafukan sada zumunta, jarumar ta hau shafinta na Twitter ta dinga fada da kumfar baki har da su dura ashariya.

To a yau kuma an wayi gari jarumar ta rubuta wani abu da ya sake jawo hankalin mabiyan na ta, jarumar ta yi rubutu a shafin na ta kamar haka: “Idan kun ga dama kuyi ta magana daga nan har ranar tashin duniya, ni dai na fadi abinda na fada, babu wani abu da zaku fada ko kuyi wanda ba ayi ba a baya…babu wani abu sabo, ni matsala ta daya ma, lokacin bumshots dinnan ban wani kile ba…ina ma yanzu ne da an ga yanga.

Bayan wallafa wannan rubutu mutane suka sake yin caa akan jarumar, sai kuma ta kara dawowa ta sake yin wani rubutun kamar haka: “Amma yanzu ma bai baci ba, duk lokacin da na bushi iska ta zaku ganni da dan kamfe da rigar nono…”

Wallafa wannan rubutu na ta keda wuya mutane suka fara yin sharhi a kansa, inda kowa yake fadar albarkacin bakinsa, daga masu addu’ar shiriya sai kuma masu tsinuwa.

To koma mene dai yayi zafi ance maganinsa Allah, wannan maganganu na jarumar duka suna da nasaba da wancan cin mutunci da tonon silili da aka yiwa babbar kawarta.

Turawa Abokai

3 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan