Zulum Ya Ba Wata Haziƙar Malamar Firamare Kyautar N100,000 Tare Da Ciyar Da Ita Gaba

13

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ciyar da Obiagelli Mazi gaba, wata malamar firamare mai matakin albashi na 12 zuwa Mataimakiyar Shugabar Firamare sakamakon samun ta a bakin aiki da misalin ƙarfe 6:30 ranar Juma’a.

Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Firamare wato SUPEB ta jihar Borno, Shettima Kullima ya isar da wasiƙar ciyarwa gaban ranar Asabar bayan da Gwamna Zulum ya amince da shawararsa.

A wata fita da ya yi ranar Juma’a don ganin yadda cibiyoyin gwamnati ke gudanar da aiki, Gwamna Zulum ya samu Misis Mazi da ƙarfe 6:30 tana jiran ɗalibanta.

Malamar, wadda ‘yar jihar Abiya ce, ta shafe shekaru 31 tana koyarwa.

Gwamna Zulum ya same ta a Sehu Sanda Kyarimi 2 Primary dake karamar hukumar Ilimi ta Jere.

Sakamakon farin ciki da sadaukarwar Misis Mazi, Gwamna Zulum ya yaba mata, sannan ya ba ta N100,000 daga aljihunsa, kuɗin da sun kusa ninka albashinta na N35,000 sau uku.

“Bugu da ƙari, Gwamna Zulum ya umarci shugaban SUPEB da ya duba matsayin aikin matar, cancanctarta (wadda NCE ne) sannan ya bada shawarar ciyar da ita gaba”, a cewar wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamna Zulum, Isa Gusau ya fitar.

“Bayan sa’o’i 24, shugaban SUPEB ya tuntuɓi gwamna, inda ya bada shawarar a ciyar da malamar gaba zuwa Mataimakiyar Shugabar Firamare.

“Kodayake matar ba jami’a ta yi ba, gogewarta ta koyarwa ta tsawon shekaru 31 da jajircewa da kuma umarnin gwamna su ne abubuwan da suka jawo mata wannan ci gaba”, sanarwar ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan