A Karon Farko An Yi Bikin Auren Turawa Guda 60 A Lokaci Guda

103

Turawan ƙasar Bostania sun shaida wani gagarumin auren Musulmai na mutane 60 daya gudana a Sarayevo babban birnin kasar.

Ƙungiyar Musulmai ta Bostania tare da hadin guiwar kungiyoyin NGO, MFS-EMMAUS su ne suka shirya wannan gagarumin bikin aure inda kasar Dubai ta dauki nauyin komai.

Angwaye da amaren a cikin shigar su ta aure sunyi matukar kyau inda aka cika harabar wajen da karatun Alkur’ani mai girma, ma’auratan sun samu kyautar kayan sawa da kuma dalar amurka dari uku ga kowannensu. Sannan an kara musu da kyautar Alkur’ani domin kara neman kusanci ga Allah.

An shirya wannan gagarumin bikin auren ne dan zaburar da matasa da suyi aure dan gina nasu iyalin. Bosnia tana daya daga cikin kasashen Balkan sannan mafi yawansu Musulmai ne da rashin aikin yi da talauci yayi musu katutu.

Mafi yawan ‘yan Bosnia sunayin aure ne kara zube ba kamar yanda addini ya tanadar ba.

Wannan yana daya daga cikin dalilin shirya wannan bikin aure bisa ga doka da kuma tsarin addinin Musulunci kamar yadda addini ya tsara.

Daya daga cikin amaren mai suna Meliha ta bayyana cewa ”wannan abu yana da matukar muhimmanci a garemu saboda munyi koyi da addini sannan muna tunanin wannan aure zai zamo shaidar mu na kasancewa ma’aurata a gaban ubangiji.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan