An Kaiwa Donald Trump Hari Har Cikin Fadarsa

105

‘Yan sanda sun kama wani matashi dauke da wuka a kofar Fadar gwamnatin Amurka ta White House, bayan da ya yi ikrarin cewa, ya je wajen ne don ya kashe shugaba Donald Trump.


Roger Hedgpeth mai shekara 25 ya tunkari wani jami’in leken asiri da ke sintiri a kofar fadar ta White House, ya ce mai, yana so ya “kashe” Shugaba Donald Trump.


“Ina dauke da wuka wacce da ita zan aiwatar da kisan,” Hedgpeth ya fada wa jami’in tsaron, kamar yadda wani rahoton ‘yan sanda ya nuna, wanda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya samu.


An kama matashin ne a jiya Asabar, ana kuma tuhumarsa da laifin yin barazana ga lafiyar wani, a cewar ‘yan sandan birinin Washington.


‘Yan sanda sun ce, an samu wuka mai tsawon inci uku 3 ½ a a cikin kube a jikin Hedgpeth, sannan an same shi da marikin bindiga.


Hukumomin tsaron sun kuma ce an garzaya da matashin zuwa asibiti domin a duba lafiyar kwakwalwarsa, sannan an karbe motarsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan