Babbar Barazana Ce Barin Yara Suna Gararamba a Titi – Aisha Bagudu

94

Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Aisha Atiku Bagudu, ta ce babban hadari ne ga arewacin kasar nan a bar yara suna gararamba akan titi ba tare da an tura su makaranta ba.


Ta kara da cewa, duk da cewa akwai wasu yankunan da ake samun masu yin bara, amma a arewacin Najeriya matsalar ta fi kamari, abin da ta kwatantan a matsayin “abin ci baya” ga yankin.


“Kada mu manta fa mu tafiya muke yi, yaran nan su ne mu gobe, idan ba mu tallafa masu ba, wata rana yaran nan sai sun sa mu kuka, ina kera ne ga kowa da ya sa hannu, a tallafawa wadannan yara. ina kallo kamar muna kan “time bomb” ne (wani abu da zai fashe,) ranar da bam din zai fashe, kowa sai ya ji jiki.”


A cewarta, akwai mukamai da yawa da ya kamata a ce ‘yan arewa sun samu, “amma sai ka ga ba mu da yaran da ke da wannan ilimi da za su samu.”


Uwargidan gwamnan ta kara da cewa, akwai wata cibiya da take jagoranta mai yawan dalibai kusan 200 wadanda ake koyawa sana’o’i daban-daban.


“Muna koyar da su, sannan ana koya masu sana’ar hannu, wadansu za su gaya miki cewa su ba sa son su yi makaranta, sun fi son sana’a.”


“Abin da mukan gaya masu shi ne, mun yarda ba za su yi makaranta ba, amma su koyi yadda za su rubuta sunansu kuma su iya karanta wa.” Ta kara da cewa.
Asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya fitar da kididdigar cewa, yara sama da miliyan 13.2 ne ke gararamba a tituna a Najeriya ba su da karatu.


Wannan ya sabawa adadin miliyan 10.5 a shekarun baya da aka gani, kuma mafi yawancinsu a arewacin Najeriya ake samun su, a cewar UNICEF.


Wannan ya sa wasu matan gwamnonin yankin na Arewa, daukan matakan rage yawan yaran da ba sa karatu da wadanda ba su da sana’o’i.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan