Zan Mayar Da Tashar NTA Kamar CNN Idan Aka Ba Ni Rancen Naira Biliyan 181 — Lai Mohammed

87

Ministan watsa labarai, Lai Mohammed, ya sha alwashin mayar da gidan talbijin din kasar nan NTA, tamkar gidan talbijin na CNN da ke Amurka idan majalisar dokokin kasar nan ta bari ya karbo rancen, kwatankwacin kusan naira biliyan ₦181.

Wasu rahotanni sun rawaito cewa ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya je gaban kwamitin da ke kula da karbo bashi a ciki da wajen kasar nan na majalisar dattawa.

Ya kara da cewa yana so su amince a karbo bashin ne daga cikin $29.96b da Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar ta amince ya karbo domin gudanar da manyan ayyuka a kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan