Patience Jonathan: Ta Kai Ziyara Fadar Shugaban Ƙasa Bayan Shekaru 5 Da Barinta

122

Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhar, ta gana da matar tsohon shugaban kasa, Dame Patience Jonathan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na fasebuk, Aisha Buhari, ta ce sun tattauna kan batutuwa da dama ciki har da rawar da mata za su iya takawa a aikin gwamnati da kuma shugabanci.

Aisha Buhari, ta kara da cewa sun tattauna akan ilimin ƴaƴa mata wanda ya kai su ga yin tsokaci akan shirin da Patience Jonathan din ke yi akan ilimin ƴaƴa mata, mai taken Women for Change.

Hakazalika Aisha Buhar, ta ce ta saurari ra’ayin matar tsohon shugaban kasar akan wadannan batutuwa, inda kuma ta kewaya da ita bangarorin fadar shugaban kasar, lamarin da ya tuna mata lokacin da take fadar.

Dame Patience Jonathan dai ita ce mai dakin tsohon Shugaba ƙasa Goodluck Jonathan wanda ya mulki kasar nan daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2015.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan