Sadio Mane Ya Fara Daukan Atisaye

107

Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kuma dan asalin kasar Senegal wato Sadio Mané ya fara yin atisaye tare da takwarorinsa na Liverpool bayan daya warke daga rainin daya samu.

Mane yaji ciwonne tun aranar 23 ga watan Janairu na sabuwar shekarar da muke ciki yayin da Liverpool take fafatawa da Southampton inda Liverpool din tayi nasara.

Asakamakon raunin da Mane dai ya rasa wasannin da Liverpool ta buga da kungiyoyin kwallon kafa na West Ham United da Southampton da kuma Shrewsbury Town.

Zakaran dan kwallon na nahiyar Afrika yaci kwallaye 11 sannan ya taimaka anci kwallaye 22 a wannan kakar ta Premier da ake fafatawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan