Sarkin Kano Sanusi II Ya Kaiwa Tsohon Hakimin Dambatta Ziyarar Ba-zata

431

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai wa Sarkin Bai Alhaji Muktar Adnan, mai shekarar 94, ziyarar ba-zata a garin Dambatta.

A cikin watan Disambar shekarar 2019 ne mai martaba Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero, ya tsige Muhktari Adnan, daga hakimcin Dambatta, bisa rashin mubaya’a

Tsohon hakimin na Dambatta da aka tsige, shi ne mamban majalisar masu naɗa Sarki a masarautar Kano mafi dadewa, wanda kuma yana daga cikin wadanda suka zabi tsohon Sarkin Kano marigayi Ado Bayero, tare da nada shi a shekarar 1963.

Haka kuma kakan Sarkin Kano na yanzu wato Sanusi I ne ya nada Sarkin Bai a shekarar 1954 a matsayin hakimin Dambatta.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan