Tsakaninmu Da Shugaba Buhari Allah Ya Isa – Idris Ahmed

362

Fitaccen mai goyon bayan shugaban ƙasa Muhammad Buhari, a kafafen sada zumunta na zamani, Dakta Idris Ahmed, ya bayyana cewa tsakaninsu da shugaba Buhari Allah ya isa.

Idris Ahmed, wanda mazaunin birnin Coventry ne da ke ƙasar Ingila, ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk.

“Tsakaninmu da shugaban kasa Muhammadu Buhari da manyan hafsoshin sojojinsa, Allah ya isa. Bamu yafe ba duniya da lahira”

Tun da farko dai Idris Ahmed, ya yi ta rubuce-rubuce akan ya sauke shugabannin rundunar sojojin kasar nan, bisa dalilin karewar wa’adinsu tare kuma da zargin rashin yin abin da ya dace akan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara musamman a yankin arewa maso gabashin ƙasar nan.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Yulin shekarar 2015 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada manyan hafsoshin tsaron kasar nan guda hudu na tsawon shekara hudu bayan shugaban ya sauke magabatansu.

Manyan hafsoshin tsaron su ne:

Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin – Babban hafsan hafsoshi.
Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai – Babban hafsan sojin kasa
Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas – Babban hafson sojin ruwa
Air Vice Marshal Sadiq Abubakar – Babban hafson sojin sama.
Air Vice Marshal Monday Riku Morgan – Shugaban rundunar tara bayanan sirri
Manjo Janar Babagana Monguno mai murabas – Mai bayar da shawara kan tsaro

A shekarar 2019 shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin hafsoshin tsaron da wata shida wanda ya kare a watan Disambar shekarar.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan