Yankin Arewa Ne Ke Da Kaso 87 Na Talakawan Ƙasar Nan – Bankin Duniya

219

A rahoton da bankin duniya ya wallafa, ya bayyana cewa yankin kudu maso kudu ne yankin da ya samu raguwar talauci tsakanin shekarar 2011 da 2016.

Sannan rahoton Ya ce: “Talauci a Arewacin ƙasar nan na karuwa musamman a yankin Arewa maso yammacin kasar.”

“Kimanin rabin masu fama da talauci na arewa maso yamma kuma kashi 87 na talakawan kasar na arewacin ƙasar nan.”

A ɗaya ɓangaren kuma rahoton ya bayyana cewa a jihohin Kano da Kaduna, da Katsina da Jigawa, da kuma Zamafara da Sokoto da Kebbi, a nan talauci ya samu gindin zama.

“Talauci a yankin kudancin ƙasar nan na matakin kashi 12. Yankin kudu maso kudu ne yanki mai karancin talauci tsakanin 2011 da 2016.”

A ƙarshe rahoton ya bayyana cewa kashi 64 na dukkan talakawan ƙasar nan su na zaune ne a yankin karkara, kuma kashi 52 na masu zama a karkara talakawa ne.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan