A Shirye Nake In Kawo Ƙarshen Ta’addanci A Najeriya- Buhari

111

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga fatan da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare ke da shi na iya kaɗa ƙuri’a a yayin zaɓukan Najeriya.

Shugaba Buhari, wanda ya yi jawabi a yayin ganawa da shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Habasha, NICE a Addis Ababa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tallafa wa tare da bada haɗin kai ga hukumomin tsaron Najeriya.

A ta bakinsa, a shirye yake da ya kare tare tabbatar da haɗin kan Najeriya.

Shugaban ya kuma yi shiru na minti ɗaya don girmama waɗanda suka rasa rayukansu ranar Lahadi a harin da ‘yan Boko Haram suka kai a ƙauyen Auno dake jihar Borno.

Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta fatattaki ta’addanci, kashe-kashe da dukkan na’ukan laifuka a ƙasar nan.

Game da zaɓen mazauna ƙasashen ƙetare, ya ce: “Na sha faɗa cewa ba na adawa da zaɓen mazauna ƙasashen ƙetare.

“Amma, kuna buƙatar ku gamsar da Majalisar Dokoki ta Ƙasa don ta gyara dokokin da za su mayar da zaɓen mazauna ƙasashen ƙetare tabbatacce”.

Bisa hanyoyin sauƙaƙa kasuwanci, Shugaba Buhari ya ce an yi masa bayanin irin wahalhalun da wasu kamfanonin Najeriya ke sha a ƙasar ta Habasha, musamman Dangote Group da Lubcon.

“Na umarci hukumomin da suka dace da su duba waɗannan batutuwa da nufin warware dukkan ƙorafe-ƙorafen da hukumomin Habasha”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan