Buhari Bai Taɓa Yin Alƙawarin Bayyana Kadarorinsa Ba- Adesina

110

A ranar Talata ne Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari bai taɓa yin alƙawarin bayyana kadarorinsa ba.

Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Femi Adesina ya bayyana haka a Abuja yayinda yake sukar matsayin Bishop Matthew Kukah a yayin gabatar da ƙaddamar da wani littafi mai suna “One Step Ahead”, littafin da tsohuwar shugabar Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’anati, EFCC, Farida Waziri ta wallafa.

Mista Kukah, wanda shi ne babban baƙo mai jawabi a wajen taron, ya ce ya ji mutane suna tambaya: “Me yasa Shugaban Ƙasa ya yi amfani da fam ɗin Bayyana Kadarori na Mai Shari’a Onnoghen wajen kafa masa hujjar cin hanci sannan ya kore shi, duk da shi ma Shugaban Ƙasar da kansa bai bayyana kadarorinsa ba kamar yadda ya yi alƙawarin a lokacin kamfen ɗinsa?”
Sai dai Mista Adesina, wanda ya yi bitar littafin, ya bada amsa da cewa: “Ina tuna cewa an naɗa ni ne ranar 31 ga watan Mayu, 2015, lokacin da na fara aiki ranar 1 ga Yuni, a wata keɓantacciyar tattaunawa da na yi da Shugaban Ƙasa, ɗaya daga cikin tambayoyin farko da na yi masa ita ce: “Wannan alƙawarin na bayyana kadarori, yaushe za ka cika shi?”
Lokacin da ya amsa min sai ya ce: “Za ka iya nuna min inda aka yi wannan alƙawarin?”

“Mun duba ko’ina amma ba mu ga inda Shugaban Ƙasa ya ce zai bayyana kadarorinsa ba”, in ji Mista Adesina.

“Kuma ya ce min: Me doka take buƙata? Doka tana buƙatar ka bayyana kadarorinka. Amma suna ta cewa ya yi alƙawarin zai bayyana kadarorinsa”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan