Ganduje Zai Ɗauki Likita 1 Aiki Daga Kowace Ƙaramar Hukuma A Kano

109

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano za ta ɗauki likita ɗaya aiki daga kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 44 don inganta kula da lafiya a jihar.

Gwamna Ganduje ya sanar da haka ne a yayin Taron Ƙoli na Kula da Lafiya a Matakin Farko na 2020 da aka yi a Kano ranar Talata.

Gwamna Ganduje ya ce a ƙoƙarinta na inganta kula da lafiya a matakin farko, gwamnatin jihar ta fara yunƙurin mayar da ma’aikatan kula da lafiya a matakin farko daga Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi zuwa Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko ta Jiha daga nan zuwa ƙarshen watan Maris.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan