Gwamnatin Buhari Za Ta Fara Hukunta Iyayen Da ‘Ya’yansu Ba Sa Zuwa Makaranta

5

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce akwai akwai yiwuwar a fara gurfanar da iyayen da ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a gaban kotu.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a jiya Talata yayin tattaunawa da wakilan Kwamitin Majalisar Wakilai na Ilimin Bai Ɗaya da Aikace-Aikace.

Ya ce daga cikin dabarun da za a yi amfani da su don kawo ƙarshen matsalar sanya yara makaranta ita ce wayar da kan masu riƙe da sarautun gargajiya da kuma ƙarfafa gwiwar gwamnatocin jihohi su zuba kuɗaɗe da yawa a ilimi daga tushe.

Ya bada shawarar da a kafa wani kwamitin-kar-ta-kwana a kan ilimi don tabbatar da cewa yara suna zuwa makaranta.

“Hana yaro samun ilimi daga tushe laifi ne ga al’umma”, in ji Mista Adamu.

Ya ce yayinda ƙasashen Afirka da dama ke ware wa ilimi kaso mai tsoka a kasafin kuɗinsu, Najeriya tana ware wa ilimi kaso 10 ne kawai cikin ɗari.

Mista Adamu ya ce an ba Ma’aikatar Ilimi N120 ta ciyar da kowane ɗalibi a makarantun haɗaka kullum, maimakon N200.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan