Idan Buhari Ya Sake Zuwa Maiduguri Sai Mun Kai Masa Hari – Abubakar Shekau

224

Shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya bada sharadin sakin sauran ‘yan matan Chibok da har yanzu suke hannunsa bayan da yayi garkuwa da su.

Sama da ƴan mata 100 ne daga cikin 276 da aka sace a makarantar sakadiren ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno tun 2014 ke hannun ‘yan Boko Haram din.

Cikin wani faifan bidiyo da Shekau din ya saki kasa da sa’o’i 24 da zuwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar Borrno, Shekau ya ce zasu saki ‘yan matan ne kadai idan gawamnatin tarayya ta saki ‘yan kungiyar da ke hannunsu a tsare.

Abubakar Shekau ya kuma buƙac Shugaba Buhari, da kada ya kuskure ya kara zuwa jihar Borno domin kuwa a cewarsa kungiyarsa a shirye take. Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari

Shekau ya ce ‘yan ta’addar za su kaiwa shugaban kasa hari matukar ya kara komawa jihar ta Borno.

Idan zamu tuna dai, mayakan Boko Haram din sun kai hari jihar sa’o”i kadan bayan da shugaba Buhari ya kammala ta’aziyyar wadanda suka kashe a Auno da ke Maiduguri a ranar Lahadi.

“Buhari ya zo Maiduguri yana ikirarin shi mutumin arziki ne. Toh kada ya kuskure ya kara yin hakan,” Shekau ya ce a

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan